Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnati ta ceto mutane 103 daga hannun 'yan bindiga - Masari

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana samun nasarar ceto mutane 103 daga hannun ‘yan bindiga, bayan shafe tsawon lokaci suna garkuwa dasu don karbar kudin fansa.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari Daily Trust
Talla

Yayin karbar bakuncin mutane 77 daga cikin wadanda aka ceto ranar Alhamis a garin Katsina, Masari yace kamar yadda aka ceto daliban makarantar sakandaren Kankara sama da 344, a wannan karon ma an kubutar da mutanen 103 ta hanyar tattaunawa kawai ba tare biyan kudi ba.

Daga cikin wadanda da aka ceto akwai mata masu shayarwa, da yara mata da shekarunsu suka kama daga 6 zuwa 16, sai kuma jami’in soja guda da kuma dan sanda.

Kafin sanarwar gwamnan Katsina dai, a ranar Alhamis rahotanni daga garin Jibiya dake jihar suka ce wata kungiya da ake kyautata zaton ta Miyetti Allah ce, ta taimaka wajen ceto wadanda masu satar mutane don karbar kudin fansa suka yi garkuwa dasu, ba tare da an biya kudi ba.

Sai dai kokarinmu na neman tabbaci daga kungiyar Miyetti Allah ya ci tura, sakamakon kaurace wa ‘yan jarida da suka yi, amma wani mazaunin Jibiya ya tabbatar da ganin motoci dauke da wadanda ake kyautata zaton sune aka kubutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.