Isa ga babban shafi
Najeriya-Katsina

Matasan Najeriya sun yi zanga-zangar bukatar ceto daliban Kankara a Katsina

Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya yau sun gudanar da zanga zangar lumana a birnin Katsina domin matsin lamba ga gwamnatin kasar wajen ganin ta kubutar da dalibai sama da 300 da Yan bindinga suka sace a makarantar Sakandaren Kankara.

Wasu matasan Najeriya da ke zanga-zangar bukatar ceto daliban Sakandiren Kankara da 'yan bindiga suka sace
Wasu matasan Najeriya da ke zanga-zangar bukatar ceto daliban Sakandiren Kankara da 'yan bindiga suka sace RFI Hausa
Talla

Matasan wadanda suka fito daga sassan arewacin Najeriya sun bayyana fushin su da matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na kin ziyarar garin Kankara domin jajantawa iyayen daliban da kuma kin cewa uffan domin kantar musu da hankali.

Shugaban tawagar matasan Nastura Ashir Sharif yace abin takaici ne yadda shugaban kasar wanda yanzu haka yake Daura a Jihar Katsina yaki nuna damuwa da halin da iyayen daliban ke ciki dangane da bacewar yaran su da kuma yin bayani ga jama’a kan kokarin da gwamnati ke yi akai.

Ministan tsaron Najeriya Bashir Magashi da Babban jami’in yada labaran ma’aikatar tsaro duk sun bayyana cewar dakarun su na iya bakin kokarin su wajen ganin an kubutar da daliban ba tare da ganin sun jikkata ba.

Iyayen daliban da dama wadanda ke Kankara sun bayana rashin gamsuwa da matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka, inda suka bukaci ganin an bi ta kowacce hanya domin kubutar da ‘yayan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.