Isa ga babban shafi
Najeriya-Katsina

Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun sakandaren kwanan dake Jihar

Gwamnatin Katsina dake Najeriya ta sanar da rufe daukacin makarantun sakandaren kwanan dake Jihar sakamakon sace wasu dalibai da ‘yan bindiga suka yi a makarantar Sakandaren Kankara daren jiya.

Allon makarantar sakataren kimiyya da Kankara dake jihar Katsina
Allon makarantar sakataren kimiyya da Kankara dake jihar Katsina Daily Trust
Talla

Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya bada wannan umurnin bayan ya ziyarci makarantar tare da manyan jami’an gwamnatin sa, inda ya gana da iyayen yara da da Sarakuna da malaman addini da kuma shugabannin tsaro kan matsalar.

Masari ya bukaci jama’ar Jihar da su kwantar da hankalin su da kuma yin taka tsan tsan, yayın da gwamnati zata yi duk abinda ya dace wajen ganin an saki daliban da aka sace.

Gwamnan yace tuni jami’an soji da Yan sanda da na tsaron farin kaya suka bazama wajen gano wadannan dalibai da wadanda suka sace su.

Masari yace gwamnatin jiha da ta tarayya na iya bakin kokarin su wajen kawo karshen ‘yan bindigar da suka addabi jihar, kumą ba zasu daga kafa kan lamarın ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.