Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da daliban sakandire a Katsina

‘Yan bindiga dauke da manyan makamai da suka kai hari garin Kankara a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sun yi awon gaba da wasu daliban sakandare a cikin daren Juma'a, zuwa wayewar garin Asabar.

Hoton da ke alamta 'yan bindiga don sukunin bada labari.
Hoton da ke alamta 'yan bindiga don sukunin bada labari. Information Nigeria
Talla

Rahotanni daga Katsinar na cewa bayan da maharan suka gama abin da suka je yi garin ne, suka dunguma cikin makarantar Sakandiren Kimiyya ta maza dake garin wato (GSSS Kankara), mallakar jihar Katsina inda suka wuce da daliban da ba a kai ga tantance adadinsu ba.

Wannan na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya sauka jiharsa ta Katsina don ziyarar kashin kansa.

‘Yan bindigar sun kuma harbi daya daga cikin jami'an tsaron da ke makarantar a wuya, inda tuni aka garzaya da shi zuwa asibiti Kankara domin ceto rayuwarsa, yayin da dayan kuma ba a san inda yake ba.

Wata majiya ta ce sai da ‘yan bindigar suka garzaya rukunin gidajen malaman makarantar, inda suka sace matar wani ma’aikacinta, sannan daga bisani suka nufi dakunan dalibai.

Majiyoyin soji sun bayyana cewa daga baya, dakarun sojin kasar sun isa makarantar don tinkarar ‘yan bindigar, amma suka arce da daliban da ba tantance adadinsu ba.

Jaridar Punch da ake wallafawa a Najeriyar ta ruwaito cewa kakakin rundunar ‘yan sandan SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma bai bayyana adadin daliban da aka sace ba, inda ya ce ana kan kidaya daliban don tantance wadanda ba sa nan.

Sai dai jaridar 'Daily Nigerian' da ake wallafawa a kasar ta ce ana fargabar cewa an sace daliban da dama da kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Wani malamin makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce dimbim iyayen dalibai ne suka isa makarantar, don sanin halin da ‘yayansu ke ciki.

Malamin ya ce bayan 'yan bindigar sun tara yaran ne, sai suka kada su zuwa kauyen Pauwa, inda suka ajiye dimbim babura.

Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da kamari a yankin arewacin Najeriya, duk kuwa da ikirarin da Hukumomi suke na cin galabar Lamarin.

Wannan na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya sauka jiharsa ta Katsina don ziyara ta kashin kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.