Isa ga babban shafi
Najeriya

Katsinawa sun karyata Zamfara kan ceto 'yan mata

Al'ummar garin Dan Aji da ke Karamar Hukumar Faskari ta jihar Katsinan Najeriya sun yi watsi da ikrarin gwamnatin Jihar Zamfara cewar, babu abin da aka biya wajen sakin 'yan mata 26 da 'yan bindiga suka sace daga Jiharsu.

'Yan matan Katsina 26 da aka ceto daga hannun 'yan bindiga a Zamfara
'Yan matan Katsina 26 da aka ceto daga hannun 'yan bindiga a Zamfara Katsina Post
Talla

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar, Sarkin Dan Aji Alhaji Lawal Dogara na cewa al’ummar garin sun biya Naira miliyan 6 da dubu 600 a matsayin kudin fansa kafin sakin 'yan matan da aka sace, inda yake cewa bai dace gwamnan Zamfara ya rika  bugun-kirjin cewar, tattaunawar da aka yi da 'yan bindigan ta kai ga sakin su ba tare da biyan kudin ba.

Sarkin Dan Ajin ya bayyana cewar wasu daga cikin shugabannin al’ummar garin Alhaji Abdulkarim Dan Aji da Liman Babangida Dan Aji suka kwashe kwanaki 3 suna takawa a cikin daji domin kai wa 'yan bindigan kudin fansar.

Su dai wadannan 'yan mata an kwashe su ne a garin ranar 13 ga watan jiya, bayan 'yan bindigan sun bi gida-gida suna zaben 'yan matan kafin su gudu da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.