Isa ga babban shafi
Najeriya

Mun halaka 'yan bindiga 100 tare da kame wasu 148 cikin watanni 2 - Sojoji

Rundunar sojin Najeriya tace, ta samu nasarar halaka akalla ‘yan bindiga 100 yayin farmakin da ta kaddamar kan sansanoninsu a sassan arewa maso yammacin kasar cikin watanni 2 da suka gabata.

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya AFP/SUNDAY AGHAEZE
Talla

Rundunar ta bayyana haka ne ta hannun mukaddashin daraktanta kan kafafen yada labarai Birgediya Janar Benard Onyeuko, yayin ganawa da manema labaran jiya asabar a jihar Katsina.

Mai Magana da yawun sojin yace bayan kaddamar da samame kan sansanonin ‘yan bindigar daga ranar 1 ga watan Yuli zuwa ga Satumban da muke, sun samu nasarar ceto akalla mutane 107 daga hannun maharan, yayinda suka kama ‘yan bindigar 148, bayaga akalla 100 da suka kashe.

Birgediya Janar Onyeuko, ya kara da cewar, dakarun Najeriyar sun kuma kame wasu mutanen 20 dake yiwa ‘yan bindigar leken asiri 20, masu yi musu safarar makamai, da sauran kayayyaki 26, dillalan shanun sata 13, sai kuma masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba 315.

A bangren dabbobi kuwa, sojin Najeriyar sun bayyana kwato shanu dubu 3 da 984, da kuma tuamakai dubu 1 da 627.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.