Isa ga babban shafi
Najeriya-Katsina

Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban sakandaren Kankara

Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin sace daruruwan daliban makarantar sakandaren kwana ta Kankara dake jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya.

Wasu mayakan kungiyar Boko Haram
Wasu mayakan kungiyar Boko Haram Defencepost
Talla

Shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ne yayi ikirarin sace daliban cikin wani sakon murya da ya fitar.

Sace daruruwan daliban makarantar a Katsina maimaicin abinda ya faru ne a shekarar 2014, lokacin da mayakan na Boko Haram a karkashin jagorancin Shekau suka sace daruruwan ‘yammatan makarantar sakandaren Chibok dake jihar Borno.

Tuni dai Gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya wato CNG, ta sha alwashin fara zaman dirshen a garin Daura da ke jihar Katsina don nunawa shugaban kasar Muhammadu Buhari damuwarsu kan abun da ya faru na sace daliban makarantan sakandare a garin Kankara.

A halin da ake ciki gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari yace dalibai 333 ne suka bata bayan farmakin ‘yan bindigar a makarantar Sakandaren ta Kankara, sai dai daga bisani gwamnan yace jami’an tsaro sun yi nasarar ceto 17 daga cikin daliban.

00:59

Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari kan ceto daliban makarantar sakandaren Kankara

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.