Isa ga babban shafi

‘Yan Najeriya na mamakin yadda Buhari bai ziyarci makarantar Kankara ba

kungiyoyi da daidaikun mutane a Najeriya sun caccaki shugaban kasar Muhammadu Buhari, biyo bayan sace daliban makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, a jihar Katsina da ke arewacin kasar a ranar Juma’a.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. businessday
Talla

Akasarin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a kan al’amarin sun ce Buhari ya gaza, kuma suna matukar mamakin cewa har yanzu shugaban bai ziyarci makarantar ba, duk da cewa a cikin jihar Katsina take, kuma yana jihar a halin yanzu.

Wadanda suka bayyana alhini da mamakinsu a kan wannan lamari dai sun hada da gamayyar kungiyoyin ‘yan arewa, Middle Belt da kuma sakataren yada labaran kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Yinka Odumakin, da kuingiyar ‘yan Neja Delta da sauransu.

Bugu da kari, a ranar Lahadi, ‘yan Najeriya da dama sun hau dandalin sada zumunta a intanet, inda suka yi ta caccakar shugaban kasar saboda rashin ziyartar makarantar.

Sai dai fadar shugaban Najeriya, ta bakin kakakinta, Malam Garba Shehu, ta ce ta mayar da hankali ne wajen warware matsalar da ake da ita a halin yanzu, tana mai cewa abin da ya sha mata kai shine ceto yaran da aka sace ba tare da bata lokaci ba.

A wata hirar tarho da ya yi da wakilin jaridar ‘Punch’ da ake wallafawa a Najeriya, kakakin fadar shugaban Najeriya, Garba Shehu ya ce ministan tsaron kasar da babban hafsan sojin kasar sun ziyarci makarantar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.