Isa ga babban shafi
Najeriya-Katsina

Boko Haram ta yada bidiyon daliban Kankara da tayi ikrarin sacewa

Kungiyar Boko Haram ta yada bidiyon 'yan makarantar sakandaren Kankara da tace mayakan ta ne suka sace, wanda ke nuna daliban na rokon gwamnati da ta rusa kungiyoyin 'yan sa kai da rufe kowacce irin makaranta, cikinsu harda makarantun Islamiya.

Daliban makarantar sakandaren Kankara dake jihar Katsina cikin hoton bidiyon da kungiyar Boko Haram ta yada
Daliban makarantar sakandaren Kankara dake jihar Katsina cikin hoton bidiyon da kungiyar Boko Haram ta yada Facebook/screenshot
Talla

A hotan bidiyon dake dauke da tarin daliban a jeji cikin itatuwa, yaran sun bayyana wasu bukatu da ake ganin wadanda suka kamą su suka sanya su magana akai.

Wata murya daga cikin wadanda suke garkuwa da yaran tace an yi wannan bidiyo ne domin nunawa Gwamnan Katsina daliban domin ganin cewar suna cikin koshin lafiya.

Mai maganar yace da ganin daliban ka san suna cikin koshin lafiya.

Dalibin da aka sa yayi magana ya roki gwamnati da ta janye sojojin da aka tura domin ceto su, domin ba za su iya yiwa mayakan komai ba, yayin da ya bukaci daina tura jirgin sama domin farautar su.

Cikin yanayin fargaba, dalibin ya sake rokon gwamnati da ta janye dakarun sojin dake nemansu tare da jiragen sama, inda yace taimakon da suke bukata daga wurin ta kenan.

Daga bayansa kuma wasu tarin dalibai da dama na cewa, kun san halin da muke ciki, ku taimaka mana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.