Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Yawan masu cutar COVID-19 a Najeriya ya zarta dubu 2

Adadin karin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya sake hauhawa a ranar Juma’a, bayanda cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta kasar ta sanar da gano masu dauke da cutar 238 a kwana 1.

MInistan lafiyar Najeriya Osagie Ehanire yayin ganawa da manema labarai a Abuja, kan halin da ake ciki kan annobar coronavirus a Najeriya. 2/3/2020.
MInistan lafiyar Najeriya Osagie Ehanire yayin ganawa da manema labarai a Abuja, kan halin da ake ciki kan annobar coronavirus a Najeriya. 2/3/2020. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Karin adadin ya sanya jimillar wadanda suka kamu da coronavirus a Najeriya kaiwa dubu 2 da 170, daga cikinsu 351 sun warke, sai kuma 68 da suka mutu.

Hukumar NCDC tace an samu karin mutanen da annobar ta harba a jihohi 22, da suka hada da Kano mai mutane 92, sai Abuja da kuma Legas, inda karin mutane 36 da kuma 30 suka kamu.

Sauran jihohin sun hada da Gombe mai mutane 16, Bauchi mai guda 10, sai 8 a Delta, mutane 6 a Oyo, sai kuma jihohin Zamfara da Sokoto masu mutane 5-5 da suka kamu, yayinda Ondo da Nasarawa ke da mutane 4-4.

Jihohin Kwara, Edo, Ekiti, Borno da kuma Yobe na da mutane 3-3 da suka kamu da cutar ta COVID-19, sai Adamawa mai mutane 2, yayinda Niger, Imo, Ebonyi, Rivers, da kuma Enugu suka bada rahoton samun mutum guda-guda da suka harbu da annobar.

Karo na biyu kenan a jere da Kano da aka samu adadi mafi yawa da suka kamu da coronavirus a Kano da mutane 92 a ranar Juma’a, sai kuma 80 a ranar alhamis.

Sai dai shugaban hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC Chikwe Ihekeazu, yace karuwar adadin masu dauke da cutar murar alakakan nada nasaba da karuwar azamar yiwa mutane gwaji, la’akari da cewar a ranar alhamis kadai, mutane dubu 2 aka yiwa gwajin cutar ta coronavirus.

A ranar talatar da ta gabata, hukumar NCDC ta sanar da aniyar yiwa mutane akalla miliyan 2 gwajin cutar coronavirus a fadin Najeriya nan da watanni 3.

Tuni dai annobar ta halaka sama da mutane dubu 235 da 500 a fadin duniya, yayinda wasu sama da miliyan 3 da dubu 303 da 510 suka kamu, daga cikinsu kuma miliyan 1 da dubu 3 da 600 sun warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.