Isa ga babban shafi
Najeriya

An tafka hasarar tarin kayan agaji a garin Rann - MDD

Babban jami’in lura da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya na jin kan ‘yan gudun hijira a Najeriya, Edward Kallon, ya koka bisa yadda aka tafka hasarar tarin kayayyakin agaji na abinci da magungunan da aka shirya rabawa ‘yan gudun hijirar da ke garin Rann a gabashin jihar Borno.

Babban jami’in da ke lura da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya na jin kan ‘yan gudun hijira a Najeriya, Edward Kallon.
Babban jami’in da ke lura da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya na jin kan ‘yan gudun hijira a Najeriya, Edward Kallon. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Mista Kallon, ya dora alhakin hasarar kayan tallafin, kan harin da mayakan Boko Haram suka kai ranar 14 ga watannan a garin na Rann, da nufin kame sansanin soji, yunkurin da bai yi nasara ba.

Sai dai jami’in na Majalisar dinkin duniya, ya ce mayakan sun yi nasarar sace tare da kone tarin kayan agaji da na magunguna da abinci, yayin farmakin.

Kimanin ‘yan gudun hijira dubu 76 da ke zaune a garin na Rann, aka tsara za su amfana daga kayayyakin tallafin.

A halin yanzu dai mafi akasarin yan gudun hijirar da suka tsere daga garin na Rann sun koma sansanin da suke, bayan kawo karshen barazanar da suke fuskanta da sojin Najeriya suka yi.

Sai dai Mista Kallon, wakilin majalisar dinkin duniyar a Najeriya, ya ce an janye ma’aikatan agajinsu 14 da ke aiki a garin na Rann, a dalilin farmakin Boko Haram na ranar 14 ga watan Janairu, kuma a halin da ake ciki ba a tsayar da lokacin komawarsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.