Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnati, NLC, da ASUU a Litinin

Gwamnatin Najeriya da shugabancin kungiyar kwadagon kasar NLC, sun amince su ci gaba da tattaunawa a ranar Litinin, don cimma matsaya ta karshe kan karin mafi karancin albashin ma’aikata.

Wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya a birnin Legas. 20/06/2007.
Wasu daga cikin 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya a birnin Legas. 20/06/2007. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Bangarorin sun yanke shawarar ce, yayin ganawar da suka yi a jiya Juma’a ta tsawon kusan sa’o’i 5, wadda bata kammala ba, kan batun na neman karin mafi karancin albashin zuwa naira dubu 30 daga dubu 18.

Tattaunawar na zuwa ne bayan da cikin makon da ya kare, kungiyar kwadagon ta NLC ta sha alwashin shiga yajin aiki na sai baba ta gani daga ranar Talata, 8 ga watan Janairu na 2019 da muke ciki, domin tilastawa gwamnati amsa bukatarta.

Tuni dai gwamnatocin jihohin Najeriya suka tsaya kan cewa baza su iya biyan Naira dubu 30 da NLC ke nema ba, sai dai naira dubu 22, da 500.

A wani labarin kuma, Ministan Kwadagon na Najeriya, Chris Ngige, ya ce, za su ci gaba da tattaunawa da shugabancin kungiyar malaman jami’o’in kasar ASUU, a wannan Litinin mai zuwa don kawo karshen yajin aikin da malaman ke yi.

A Yau Asabar Ministan Kwadagon Najeriyar ya bayyana haka cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Ranar 5 ga watan Nuwamban da ya gabata, malaman jami’o’in Najeriyar suka soma yajin aiki, kan wasu bukatu da dama, wadanda ke kunshe cikin yarjejeniyar da suka cimma da gwamnatin kasar a shekarar 2009.

Wasu daga cikin bukatun sun hada da neman kara yawan kudaden gudanarwa da gwamnati ke baiwa jam’o’in tarayya, da kuma tabbatar da cewa ana baiwa jami’o’i mallakar jihohi isassun kudaden bunkasa su.

Ganawar ta ranar Litinin za ta zama kashi na uku, la’akari da cewa a ranar 15 ga watan Nuwamba, Ministan Kwadagon Najeriyar ya gana da kungiyar ta ASUU, sai kuma ranar 17 ga watan Disamba, duk dai domin kawo karshen yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.