Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta tsaida Atiku a matsayin dan takararta a zaben 2019

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasar da za’ayi a shekara mai zuwa.

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP a zaben 2019.
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP a zaben 2019. REUTERS/Paul Carsten
Talla

Wannan nasara zata bashi damar fafatawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC mai mulki, wanda ya kada shi a irin wannan zaben fidda gwanin na Jam’iyyar APC shekaru 4 da suka gabata.

Bayan kamala zaben da aka kwashe daren jiya ana kada kuri’u, aka kuma kidaya su a bainar jama’a, tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya yiwa daukacin yan takarar fintinkau wajen samun kuri’u 1,532, yayin da wanda ya zo na biyu, wato Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya samu kuri’u 693, sai kuma shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da ya samu kuri’u 317 a matsayi na 3.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya samu kuri’u 158 ya kuma zo na 4, sai Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo da ya zo na 5 da kuri’u 111.

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya zo na 6 da kuri’u 96, sai Ahmad Makarfi mai kuri’u 74, Kabiru Turaki mai kuri’u 65, Attahiru Bafarawa mai kuri’u 48, David Mark kuri’u 35, Jonah Jang mai kuri’u 19 sai kuma Datti Ahmed mai kuri’u 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.