Jiga-jigan PDP sun yi zanga-zanga a Abuja
Shugabannin Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja don nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben gwamnan jihar Osun.
Wallafawa ranar:
Shugabannin da suka hada da Bukola Saraki, Kakakin Majalisar Dattawan kasar da Yakubu Dogara, Kakakin Majalisar Wakilai da Uche Secondus, shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, su ne suka jagoranci zanga-zangar a shalkwatan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC.
Sauran mahalarta zanga-zangar sun hada da Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido da kuma Sanata Dino Melaye.
Masu zanga-zangar na bukatar INEC ta ayyana dan takarar PDP , Ademola Adeleke a matsayin wanda ta lashe zaben na jihar Osun.
Tuni dai INEC ta ayyana Ogboyega Oyetola na APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na makon jiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu