Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Ambaliyar ruwan bana ka iya haifar da karancin shinkafa a 2019

Gwamnatin Najeriya, ta yi gargadin mai yiwuwa a fuskanci karancin wadatar shinkafa a sassan kasar, sakamakon gagarumar ambaliyar ruwan bana da ta aukawa akalla jihohi 14.

Wani manomin shinkafa yayin aiki a gonarsa dake jihar Bauchi a tarayyar Najeriya. 2 ga Maris, 2017.
Wani manomin shinkafa yayin aiki a gonarsa dake jihar Bauchi a tarayyar Najeriya. 2 ga Maris, 2017. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin gargadin na ranar Alhamis a garin Abuja, ministan albarkatun noma da raya karkara na Najeriya, Audu Ogbeh, ya ce idan har ba’a yi gaggawar daukar matakin sake shuka shinkafar da ambaliyar ruwan bana ta lalata ba, za’a fuskanci karancinta a cikin shekarar 2019.

Ministan ya ce jihohin da ambaliyar bana tafi shafa, wadanda sune kan gaba wajen noman shinkafa a Najeriya, sun hada da Kebbi, Jigawa, Kogi da kuma Anambra.

Ogbeh ya ce domin daukar matakan rigakafi a nan gaba, kwararru a cibiyar bincike da inganta iri ta Najeriya, sun dukufa wajen samar da ingantaccen irin shinkafa na ‘Faro 66 da Faro 67’ wadanda suke jurewa fuskantar ambaliyar ruwa, domin baiwa manoman Najeriya su shuka a wadace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.