Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnonin Najeriya sun yi afuwa ga fursunoni 340

Wasu Gwamnonin Najeriya hudu sun yi afuwa ga fursunoni akalla 340 albarkacin cikar kasar shekaru 58 da samun ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya.

An yi wa fursunoni afuwa albarkacin cikar Najeria shekaru 58 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka
An yi wa fursunoni afuwa albarkacin cikar Najeria shekaru 58 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka Florian Gaertner/Photothek via Getty Images
Talla

Gwamnonin sun hada da Abubakar Bello na Niger da Nasir El-Rufa’i na Kaduna da Simon Lalong na Filato da kuma Muhammadu Bindow na Adamawa.

Gwamna Bello ya yi afuwa ga fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa, yayin da ya sassauta wa wasu hukuncin kisa zuwa hukuncin zaman gidan kaso na wani dan lokaci.

Gwamnan ya kuma sallami wasu fursunoni 40 tare da bada umarnin biya wa fursunoni 221 tarar da aka ci su na kudade.

Shi kuwa Gwamna El-Rufai na Kaduna, ya yi afuwar ne ga fursunoni 24 da suka hada da wadanda aka yanke wa hukucin kisa kamar yadda ya shaida wa jama’a a yayin faretin da ya gudana a filin wasa na Ahmadu Bello da ke jihar don tunawa da ranar samun ‘yancin.

A can Adamawa kuwa, Gwamna Bindow ya yi afuwa ga mutane 22 kamar yadda sanarwar d ta fito daga Kwashinan Yada Labarai, Ahmad Sajo ya bayyana, yayin da Gwamna Lalong na Filato ya yi afuwa ga fursunoni 7 albarkacin wannan rana ta 1 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.