Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na bikin cika shekaru 52 da samun ‘yancin kai

Yau Nijeriya ke bikin cika shekaru 52 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallakar Britaniya. Nigeria ta samu yancin kai ne a ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 1960.Bayan karbar ragamar tafi da kasar, a matsayin Firaminista, Sir Abubakar Tafawa Balewa,a lokacin ya bayyana cewar, "Kalamai basu iya bayyana farinciki na da annashuwa ba a wannan rana, yau Najeriya ta zama 'yancacciyar kasa mai cin gashin kanta kamar takwarorinta a duniya."  

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A dai jiya ne hukumomi a kasar ta Najeriya su ka bayar da hutun kwana daya domin yin shagulgulan cika shekaru 52, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar kula da harkokin ckin gida ta fitar.

Sanarwar wacce Sakatariyar ma’ikatar, Nwaobia Daniel ta saka hanu ta fadi cewa Shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya yi kira ga ‘yan kasar da su cigaba da yin addu’a domin a sami wanzuwar zaman lafiya mai dorewa.

Matsalar tsaro baya ga cin hanci da rashawa da ke addabar kasar, na daya daga cikin kalubalan da ke barazana ga kasar ta Najeriya, a yayin da fadan addini da kabilanci ke kara lalata abubuwa a kasar.

A lokacin bikin cika shekaru 50, a shekarar 2010, wasu bam bamai a suka tashi a kusa da harabar Eagle Sqaure inda a nan akan gudanar da bikin, su ka kuma yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, a yayin da wasu da dama suka jikkata.

Hakan ya shekarar da ta gabata, saboda matsalar tsaro aka mayar da gudanar da bikin, fadar shugaban kasar.

A wannan shekarar ma, bikin cika shekaru 52, za a yi shi ne a fadar shugana kasar kamar yadda wata sanarwa daga Mai bawa shugaban kasar shawara akan harkokin sadarwa, Reuben Abati, ta fada.

Ana sa ran mataimakin shugaban kasar, Namadi Sambo, da Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark da Kakakin Majalisar Wakilai Aminu Tambuwal, da kuma babban Mai Shari’ar kasar, Justice Aloma Mukhtar za su halarci bikin a fadar shugaban kasar.
 

Har ila yau, tsofaffin shugannin kasar, a cewar Abati, da manyan jami’an gwamnati da kuma ‘Yan siyasa tare da Jakadun kasashen daban daban ne za su halarci bikin a yau.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.