Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun fatattaki mayakan Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya ta ce, ta yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram da suka yi kokarin kaddamar da farmaki a yammacin jiya Alhamis a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.

Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar
Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Rohatanni na cewa, mazauna yankin da lamarin ya faru sun yi ta jin karar harbe-harben bindiga, abin da ya razana su har suka fice daga gidajensu.

Shugaban Rundunar Operation Lafiya Dole a yankin arewa maso gabashin Najeriya, Rogers Nicholas, ya fitar da wata sanarwa, in da ya tabbatar da fatattakar mayakan.

Sanarwar ta ce, yanzu haka sojojin na ci gaba da aikin sintiri a sassan Jidari da ke birnin na Maiduguri, in da lamarin ya faru.

Sanarwa ta kuma bukaci jama’ar da suka kaurace wa gidajensu da su koma, sannan kuma su tsegunta wa jami'an tsaro duk wani motsi na mutanen da ba su amince da takunsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.