Ana wata arangama tsakanin Sojin Najeriya da Boko Haram a Maiduguri
Rahotanni daga Maidugurin Najeriya sun ce yanzu haka mayakan boko haram na fafatawa da sojojin kasar a kokarin su na kutsa kai zuwa cikin birinin da nufin kaddamar da hare-haren ta'addanci.
Wallafawa ranar:
Bayanan da ke fitowa daga garin sun ce, ana ta jin karar musayar wuta tsakanin bangarorin biyu tun karfe 6 na yamma, kuma rahotanni sun ce mayakan na kokarin kutsawa ne cikin barikin sojin Giwa inda ake tsare da kwamandodin su da dama.
Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa daga rundunar sojin kasar kan halin da ake ciki, amma kuma mazauna garin da dama sun shaida mana cewar suna cikin halin fargaba sakamakon arangamar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu