Isa ga babban shafi
Najeriya

Secondus ya bukaci gwamnatin Najeriya ta biya shi diyya

A Najeriya, shugaban jam’iyyar adawa ta PDP na kasar Mista Uche Secondus ya bukaci gwamnatin kasar ta nemi afuwarsa, tare da biyanshi diyyar naira Biliyan daya da rabi, sakamakon sanya sunansa cikin jerin wadanda ta tona asirin suna daga cikin wadanda suka wawure dukiyar ‘yan Najeriya.

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Mista Uche Secondus.
Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Mista Uche Secondus. Daily Post
Talla

Jerin sunayen da Ministan yada labaran Najeriya Lai Muhd ya bayyana, ya nuna cewar Secondus ya amshe tare da dafe naira miliyan 200 daga ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara akan tsaro na gwamnatin baya, a ranar 19 ga watan Fabarairu a 2015.

Kan haka ne shugaban Jam’iyyar adawa ta PDP ya bai wa Ministan yada labaran Najeriyar wa’adin sa’ao’i 48, da ya janye kalamansa tare da neman afuwa a bainar jama’a, ko kuma ya fuskanci matakin shara’a.

Lauyan Mista Secondus Emeka Etiaba, ya ce muddin Lai Muhammad ya ki neman afuwarsu, zasu garzaya kotu don neman hakkinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.