Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka mutane 6 a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta tabbatar da mutuwar mutane shida, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Jema’a.

Jami'an 'Yan sandan Najeriya.
Jami'an 'Yan sandan Najeriya. Reuters
Talla

‘Yan bindigar su kai harin ne a yankin Bakin Kogi da ke masarautar Kanikon da ke karamar hukumar ta Jema’a, inda suka hallaka maza 4 da mata 2, tare da raunata wasu mutanen 4.

Kakakin ‘yan sandan jihar ta Kaduna Aliyu Mukhtar ya ce a halin yanzu, hadin gwiwar sojoji da yan sanda suna kan farautar ‘yan bindigar.

A shekarar da ta gabata Jihar kaduna ta yi fama da hare-haren ‘yan bindiga musamman a yankin Birnin Gwari, dalilin da ya sanya aka girke sojoji da ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro a yankunan da matsalar ta shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.