Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bukaci hadin kan Sarakunan gargajiya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin tabbatar da shirin gwamnatinsa na kawo karshen tashe tashen hankula, da hare-haren da ake samu a sassan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Buhari wanda ya jaddada alwashin, a garin Jos yayin ziyarar da ya kai jihar Filato, ya bukaci masu rike da Sarautun gargajiya su jajirce wajen bada gudunmawar kawo karshen samun rikici, musamman tsakanin manoma da makiyaya.

Shugaban Najeriyar wanda a Juma’a ke ziyara a jihar Benue, ya ce Sarakunan gargajiya na da gagarumar gudunmawar da zasu bada wajen magance wannan matsala da wasu bata gari suka shirya aukuwarta, kasancewar kafin wannan lokaci, manoma da makiyaya sun shafe kusan shekaru 250, suna amfanar juna ba tare da samun irin wannan matsala ba a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.