Isa ga babban shafi
Najeriya

Iyayen daliban Dapchi zasu shiga kungiyar 'Bring Back Our Girls'

Wasu iyayen daliban makarantar ‘yan matan Dapchi da ake zargin mayakan Boko Haram da sacewa, sun bayyana aniyar shiga cikin kungiyar Bring Back Our Girls da aka kafa bayan sace ‘yan makarantar Chibok, a wani yunkurin na tabbatar da maido musu da ‘ya’yansu.

Wasu daga cikin daliban makarantar sakandaren Dapchi da suka tsira daga harin da wasu mayakan Boko Haram suka kai kan Makarantarsu. 22 ga Fabarairu, 2018.
Wasu daga cikin daliban makarantar sakandaren Dapchi da suka tsira daga harin da wasu mayakan Boko Haram suka kai kan Makarantarsu. 22 ga Fabarairu, 2018. REUTERS/Ola Lanre
Talla

Shugaban wani kwamiti da iyayen daliban makarantar da Dapchi suka kafa, Bashir Alhaji Mu’azu wanda shi ma ‘yar sa Fatima bashir ta bata, ya ce sun tattara sunayen yaran da aka sace 105, kuma zasu mika sunayen ga kungiyar fafutuka ta Bring Back Our girls da ke Abuja.

Karo na farko kenan da mayakan Boko Haram suka sace dalibai masu yawa tun bayan daliban makarantar sakandaren Chibok sama da 270 da suka sace a shekarar 2014.

Kiran suna da nufin tantance daliban makarantar ta Dapchi da aka yi a ranar Talata, ya nuna akwai dalibai 91 da ba’a gansu ba.

Wata daliba Amina Usman, mai shekaru 15, tana daga cikin daliban makarantar ta Dapchi da suka tsallake rijiya da baya.

Amina ta ce tana tsaka da wanke kayanta ne, a lokacin da suka ji karar harbe-harbe, tare da hangen gungun mayakan da ake zargin na Boko Haram ne suna tunkaro su a mota cikin kakin soji.

Dalibar ta ce a lokacin da suka farga cewar hari aka kawo musu ne suka fantsama cikin jeji, daga bisani ne ta hadu da daya daga cikin malamanta da kuma wasu daliban da suka tsere.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.