Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kadu da bacewar 'yan matan sakandiren Dapchi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajantawa iyayen 'yan matan sakandiren Dapchi a jihar Yobe da mayakan kungiyar Boko haram suka sace ranar litinin din makon. Kalaman shugaban wanda ke zuwa bayan kwanaki 4, da wannan ibtil'i na cewa gwamnati za ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an kubutar da su. 

Shugaban Najeriyar ya ce an sanya jirage su rika shawagi har na tsawon sa'ao'i 24 a yankin da abin ya faru duk dai daga cikin matakan da ake dauka na ganin an kubutar da 'yan matan.
Shugaban Najeriyar ya ce an sanya jirage su rika shawagi har na tsawon sa'ao'i 24 a yankin da abin ya faru duk dai daga cikin matakan da ake dauka na ganin an kubutar da 'yan matan. Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Talla

A jawaban da ya gabatar cikin kaduwa, shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari  ya ce ya damu matuka bayan samun labarin sace 'yan matan yana mai cewa tuni ya aike jakadu na musamman don jajantawa iyayen 'yan matan, baya ga umartar jami'an tsaro da su dauki matakan gaggawa don ganin an kubutar da 'yan matan.

Haka zalika Shugaban Najeriyar ya ce an sanya jirage su rika shawagi har na tsawon sa'ao'i 24 a yankin da abin ya faru duk dai daga cikin matakan da ake dauka na ganin an kubutar da 'yan matan.

Sace 'yan matan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyoyin fararen hula a Najeriyar ke ci gaba da matsa lamba ga gwamnatin Muhammadu Buharin don tabbatar da ganin an kammala kubutar da 'yan matan Sakandiren Chibok da aka sace kusan shekaru hudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.