Isa ga babban shafi
Najeriya

Akwai Alamun Za'a Gano 'Yan Matan Makarantar Dapchi Da Boko Haram Suka Sace

Wasu Bayanai daga Jihar Yoben Najeriya na nuna cewar akalla dalibai mata sama da 90 har yanzu ba’a ji duriyar su ba, bayan harin da kungiyar boko haram ta kai garin Dapchi  ranar litinin.Sai dai wani labari da dumi-dumi yammacin Laraba da muke kokarin tantancewa na nuna cewa watakila an sami kubutar da 'yan matan, domin majiyoyi masu tushe na nuna cewa motar da 'yan Boko Haram suka kwashi 'yan matan ta lalace a hanya kuma jamian tsaro suka yi nasarar kwace 'yan matan

Ayarin wasu Dakarun dake aiki tare da sojan Najeriya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya
Ayarin wasu Dakarun dake aiki tare da sojan Najeriya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya rfi
Talla

Majiyoyin samun labarai na cewa  yanzu haka jami’an tsaro da kuma shugabannin makarantar na ci gaba da tattara alkaluman daliban da aka gani, yayin da aka sanar da rufe makarantar da kuma tura daliban zuwa gidajen su.

Mun yi iya bakin kokarin mu domin jin ta bakin gwamnatin Jihar Yobe amma abin ya ci tura.

Sai dai wata sanarwa da sa hannun Babban Sakatren Labarai na Gwamnan Jihar Yobe Abdullahi Bego na gaskata cewa ana kokarin kubutar da daliban makarantar kusan 50 da ba'a  gansu ba.

A tattaunawa da wata dalibar makarantar mai suna Yagana ta bayyana cewa sun wahala a lokacin da 'yan Boko  Haram suka shiga makarantar, domin sun yi ta tserewa ne dazuka.

Ta ce suna zaune a makaranta sai suka fara jin harbe-harben bindigogi daga cikin gari na zuwa kusa da makarantar.

Wasu sun zaci injin wutan lantarki ne ya tarwatse kamar yadda aka saba gani a garin.

Cikin kankanin lokaci, tace sai suka ji harbe-harben na ta karuwa sai dalibai suka fito daga dakunansu suka fara guje-guje.

Yagana ta ce cikin lokaci kadan makaranta fashe kowa ya kama gabansa, babu wanda ya san inda zai kwana.

'Dalibai babu wanda ya kwana acikin makaranta' a cewar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.