Isa ga babban shafi
Najeriya

Turawan da aka sace a Kaduna sun kubuta

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce an saki turawan da aka sace, bayan kwanton baunar da wasu gungun masu garkuwa da mutane suka yi musu a kan hanyar Kagarko zuwa Kwoi da ke jihar Kaduna.

Jami'an 'yan sandan Najeriya na musamman masu yaki da fashi da makami da sauran manyan laifuka.
Jami'an 'yan sandan Najeriya na musamman masu yaki da fashi da makami da sauran manyan laifuka. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A ranar Talatar makon da ya kare, wasu gungun mutane suka sace kwararrun jami'an kan samar da makamashin hasken rana, da suka hada da turawan Amurka biyu, da na Canada biyu, yayin da suke kan hanyar komawa Abuja, bayan ziyarar aiki da suka kammala a kafanchan.

Gungun masu garkuwa da mutanen suka hallaka 'yan sanda biyu da ke bai wa turawan tsaro, kafin su yi awon gaba da su a waccan lokacin.

A lokacin da yake tabbatar da kubutar turawan, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Mukhtar Hussaini Aliyu, ya ce jami’an tsaro sun kama wasu mutane biyu a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadanda ake kyautata zaton da hanunsu wajen sace Turawan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.