Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Za'a kafa cibiyar 'yan sanda ta musamman a Kafanchan

Babban Sifeton rundunar ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ce nan bada dadewa ba, za’a kafa wata cibiyar rundunar ‘yan sanda ta musamman a garin Kafanchan da ke kudancin jihar Kaduna, a arewacin kasar, domin magance sake barkewar rikici nan gaba a yankin.

Babban Sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya.
Babban Sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya.
Talla

Sifeto janar din ya bayyana haka ne, yayin ziyarar da ya kai yankin da aka samu barkewar rikici a garin na Kafanchan.

A cewar babban Sifeton, tuni aka kafa wani kwamiti da zai yi bincike kan aukuwar rikicin a kudancin Kaduna, inda aka yi da’awar sama da mutane 800 aka hallaka a cikinsa.

Zalika Sifeto Idris, ya bayyana rashin jin dadi kan yadda ya ce a wasu na kambama girman rikicin da ya auku a garin na Kafanchan fiye da yadda al’amarin yake.

Ya bukaci jagororin yankunan da ke kudancin jihar Kaduna da su kara kaimi wajen taka rawar dawo da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mazauna yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.