Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Sanda Najeriya sun dakile tarzomar Kafanchan

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce, ta yi nasarar dakile wata zanga zangar da ta kusan haifar da tarzoma a garin Kafanchan na Jihar Kaduna da ke arewacin kasar. 

'Yan sandan jihar Kaduna ta Najeriya sun dakile wata zanga-zanga da ta kusan rikidewa zuwa tarzoma a garin Kafanchan
'Yan sandan jihar Kaduna ta Najeriya sun dakile wata zanga-zanga da ta kusan rikidewa zuwa tarzoma a garin Kafanchan
Talla

A jiya ne dai wasu matasa suka gudanar da zanga-zangar saboda yadda Fulani makiyaya ke kai musu hari a kauyukansu.

Kakakin 'yan sandan jihar, ASP Aliyu Usman ya shaida wa RFI hausa cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yi tattaki zuwa Kafanchan don samar da masalaha.

ASP Aliyu ya ce, an yi nasarar dakile zanga-zangar don ganin cewa ba ta kai ga kashe-kashe ko kuma lalata dukiyoyin al’umma ba.

Kakakin ya musanta zargin cewa, ‘yan sanda na wurin a lokacin da aka fara zanga-zangar har aka fasa shaguna guda takwas ba tare da sun tabaka komai ba.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.