Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaro sun musanta samun yamutsi a Kaduna

Rundunar ‘Yan sanda ta jihar Kadunam ta musanta rahotannin samun barkewar tashin hankali a Gidan Waya, a karamar hukumar Jema’a da ke jihar.

Wasu Jami'an rundunar 'yan sanda ta Najeriya
Wasu Jami'an rundunar 'yan sanda ta Najeriya
Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ASP Aliyu Usman, ya ce wasu marasa son zaman lafiyar al’umma ne kawai ke yada jita-jitar.

A satin da ya gabata, gwamnatin jihar Kaduna ta kafa dokar hana zirga zirga a karamar hukumar ta Jema’a, bayan halaka mutane akalla 20, da wasu ‘yan bindiga suka yi, wadanda ake zargin Fulani ne makiyaya, a garin Godogodo.

A waccan lokacin dai wadanda suka tsira da rayukansu, sun ce an kona gidaje da dama da ke garin, lamarin da ya haifar da zaman fargaba tsakanin Hausa/Fulani da kuma mazauna yankin.

A halin yanzu dai rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ta bukaci jama’a su cigaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba cikin bin doka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.