Gwamnatin Borno ta kara tsawaita dokar hana zirga-zirga
Gwamnatin Jihar Borno ta kara tsawaita wa’adin dokar hana zirga-zirga da ta kafa daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe.
Wallafawa ranar:
Kwamishinan yada labaran jihar Dr Muhammad Bulama ne ya bada sanarwar, wadda ta ce an kara wa’adin dokar da tsawon kwanaki bakwai, wato zuwa ranar 20 ga watan Janairu da muke ciki.
Karo na uku kenan da gwamnatin Jihar ta Borno ke kara wa’adin, bisa shawarar rundunar sojin Najeriya.
Sanarwar ta ce, an dauki matakin ne domin bai wa rundunar sojin Najeriya karin lokaci, domin daukar matakai na karasa murkushe duk wata barazanar tsaro da ragowar mayakan kungiyar Boko Haram ka iya haifarwa a yankin.
Gwamnatin Bornon ta kuma nemi afuwar, jama’ar da matakin ya shafa, dangane da matsi ko takura da dokar zata haifar musu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu