Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya ja hankalin ‘yan Najeriya a jawabansa na sabuwar shekara

A Jawabansa na shiga sabuwar shekara shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya alkawarta sanya kafar wando daya da mutane da suka haifar da tsananin wahalar man fetir da ya durkusar da hidindimun al’ummar kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaba Buhari da ke nuna takaicinsa da wahalhalun da aka jefa ‘yan Najeriya a wannan lokaci na bukukuwan sabuwar shekara ya ce zai bi didigin lamarin domin kaucewa sake aukuwar haka a nan gaba.

Jami’an gwamnatin Buhari sun sha dora alhakin wannan matsalar ta man fetir da ake fama da ita kusan wata guda kan dillalan man.

Zalika cikin jawaban nasa Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce a wannan sabuwar shekara ta 2018 za a daina shigar da shinkafar waje kasar.

A cewar shugaban shekaru biyu da suka gabata ne ya bukaci al’umma su rungumi noma kiran kuma a halin yanzu ya yi farin cikin ganin irin ci gaban da aka samu a kokarin sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya daga dogaro kan danyen mai kawai.

Sauran batutuwan da Shugaban ya tabo sun hada da sha’anin bunkasa wutan lantarki, aikin layin dogo daga Lagos zuwa Kano da gyaran manyan tittunan kasar.

Shugaba Buhari ya yi kiran zaman lafiya da kaucewa rikicin kabilanci ko addini da Siyasa. Shugaban ya kuma jadada matsayin gwamnatinsa na karya lagon mayakan Boko Haram da ke barazana a arewacin kasar.

Dangane da batun sake fasalta tsarin tafiyar da mulkin kasa kuwa shugaba Muhammadu Buhari ya ce babu wani tsari ko dokar dan adam da ba ya tattare da kura-kurai.

Buhari ya ce 'yan Najeriya zasu iya zama masu matukar gaggawa wajen kokarin samar da ci gaba, fiye da karfi ko damar da yanayin kasar ke ciki, sai dai a ra'ayinsa, matsalolin Najeriya suna da alaka ne da rashin bin doka amma ba tsarin tafiyar da mulki ba.

Kan haka ne ya bukaci da a bai wa tsarin da kasar ke kai isasshen lokaci kafin kai wa matsayin da ake bukata na ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.