Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yi alla-wadai da harin mujami’a a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kazamin harin da aka kai wata mujami’a da ke Ozubulu kusa da birnin Onitsha a Jihar Anambra wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 da jikkata 18.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Fadar shugaban ta bayyana harin a matsayin kisan gillar da aka yiwa masu ibada.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Anambra, Garba Umar, ya tabbatar da adadin a harin da ake danganta shi da zargin yunkurin kisan kai tsakanin wasu ‘Yan uwa biyu mazauna Afirka ta kudu.

Mista Garba ya kuma yi watsi da jita-jitar danganta harin da Boko Haram tare da bukatar al’ummar yankin su ci gaba da gudanar da ayukansu.

Sai dai har zuwa wannan lokaci babu wani kame da aika aiwatar kan wadanda ake zargi da hannu wajen kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.