An cafke mutane 45 bisa zargin shirya kai harin ta'addanci a Lagos
Jami’an tsaro a Lagos da ke tarayyar Najeriya sun cafke mutane 45 da ake zargi da yunkurin kai hare-haren ta’addanci a birnin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya jiyo daga bakin wasu manyan jami’an tsaro a jihar na cewa, an cafke mutanen ne a daidai lokacin da suke yunkurin kai hare-hare a Dolphin Estate da ke unguwar Ikoyi wadda ta kunshi manyan attajirai a birnin.
A cikin wata daya da ya gabata, hukumar ‘yan sandan ciki wato DSS ta sanar da kama sama da mutane 60 a Lagos wadda ita ce babbar cibiyar tattalin arziki da kasuwanci a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu