Isa ga babban shafi
Najeriya-Legas

Mutane kusan 30 suka mutu a hatsarin mota tsakanin Lagos zuwa Ibadan a Najeriya

Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo dake Najeriya ta sanar da cewa mutane akalla 26 suka mutu a wani mummunar hatsarin mota jiya tsakanin Lagos zuwa Ibadan. 

Gwamnan Jihar Lagos a Najeriya Akinwumi Ambode
Gwamnan Jihar Lagos a Najeriya Akinwumi Ambode rfi
Talla

Kunle Ajisebutu, kakakin rundunar ya kara da cewa akwai wasu mutanen 11 da suka hada da yara kanana da suka sami mumamam raunuka.

Ya ce an kwashe gawarwakin zuwa dakin ajiyan gawa dake manyan asibitocin garin  Ibadan.

Ganau sun bayyana cewa motocin fasinja biyu ne suka yi karo gaba-da-gaba kuma nan take suka kama da wuta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.