Matsalar Karancin Man Fetur Yayi Kamari a Nigeria
Rahotanni daga sassan Nigeria na cewa ana ci gaba da fuskantar matsanancin karancin man fetur, inda ake samun dogayen layukan ababan hawa a gidajen sai da mai, yayin da wasu masu ababan hawa suka maida motocin su wuraren da suke kwana a harabar gidajen sai da man fetur.
Wallafawa ranar:
Manyan biranen kasar musamman Lagos, Ibadan, Enugu da Yanagoa, da sauran garuruwan dake arewacin kasar, bayanai na nuna lamarin ya yi kamari sosai.
Farashin da ake sayarwa a kasuwannin bayan fage kan nunka kayyadadden farashin har sau hudu.
Gwamnatin kasar taki fitowa da bayanai na takamaiman dalilan da suka haddasa wannan matsala.
Wasu masu lura da lamurran kasar kan rika dora laifin kan rashin zama cikin kasa da Shugaba Muhammadu Buhari baya yi domin ya tunkari matsalolin sosai duk da cewa shine Ministan Harkokin Man Fetur.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu