Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyoyin Fararen hula sun bukaci Buhari ya tafi hutu

Wasu Shugabannin kungiyoyin fararen hula a Najeriya sun bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya gaggauta karbar hutu dan kula da lafiyar sa, kamar yadda likitocin sa suka ba shi shawara.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya dawo daga jinyar farko a kasar Ingila
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya dawo daga jinyar farko a kasar Ingila Presidential Office/Handout via REUTERS
Talla

Wata sanarwar da suka sanyawa hannu ta nuna yadda suke yiwa shugaban fatar alkhari da kuma fatar ganin ya kula da lafiyar sa.

Cikin wadanda suka sanya hannu akan sanarwar harda Lauya Femi Falana da Debo Adeniran da Chom Bagu da Cris Kwaja da Y.Z Yau da Ezenya Nwagu da Awwal Musa Rafsanjani.

Tun bayan dawowarsa daga jinya a kasar Ingila a ranar 10 ga watan maris da ya gabata, shugaban Muhammadu Buhari ya rage fitowa bainar jama’a ko kuma halartar taruka.

'Yan Najeriya dai na ci gaba da bayyana Furgaban sanni hakikane gaskiyar koshin lafiyar Shugaban.

To sai dai, a cewar mai taimaka wa Buhari  kan harakokin sadarwa Malam Garba shehu ya ce bai kamata jama’a su tayar da hankulansu ba domin kuwa shugaban na cikin koshin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.