Isa ga babban shafi
Najeriya

Sankarau: Alkaluman Mamata ya kai 438 a Najeriya

Hukumomin Najeriya sun ce kawo yanzu Alkaluman mutane da annobar Sankarau ta kashe a kasar sun kai 438.

Mutane 438 sankarau ta kashe a Najeriya
Mutane 438 sankarau ta kashe a Najeriya
Talla

Jami’in cibiyar da ke hana yaduwar cututtuka ta kasa John Oladejo, da ke tabbatar da haka a rahotan da ya fitar ya ce mamata sun fi yawa a jihar Zamfara.

Yanzu dai ciwon ya yadu zuwa jihohi 19 da ke kasar, yayin da gwamnati ke cewa an kaddamar da rigakafi.

A ranar 5 ga watan Afrilu wannan shekarar, mutane 3959 aka tabbatar na dauke da cutar, yayin da 181 aka kebe su.

Rahotanni sun ce mutane na cuncurundo a Zamfara inda cutar tafi yaduwa domin karban rigakafi.

Cutar sankarau na wannan lokaci daban ya ke da wanda aka saba gani a Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.