Isa ga babban shafi
Najeriya

Tawagar kwamitin tsaro na MDD ta kai ziyara Borno

Wata tawagar kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ta kai ziyara garin Maiduguri domin nazartar halin da ake ciki game da yaki da ta’addanci a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

'Yan gudun hijira da ke sansanin muna a Jihar Borno.
'Yan gudun hijira da ke sansanin muna a Jihar Borno. REUTERS/Paul Carsten
Talla

Karo na farko kenan da kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniyar ke kai ziyara zuwa yankin arewa maso gabashin Najeriya da ke fama da rikicin Boko Haram.

Babban makasudin ziyarar shi ne tattaunawa da hukumomin kasar a matakin jiha da tarayya, rundunar sojin kasar da kuma shugabannin ‘yan gudun hijira.

Kafin isa Jihar Bornon dai tagawar kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya ziyarci kasashen Nijar, Chadi, da kuma Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.