Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta mikawa Gwamnatin Najeriya kudadden Andrew Yakubu

Wata Kotu a birnin Kano da ke Najeriya ta mallakawa Gwamnatin kasar Dala miliyan kusan 10 da aka samu a gidan tsohon shugaban kamfanin man kasar Andrew Yakubu da kuma wasu Fam 74,000.

Tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC a Najeriya Andrew Yakubu
Tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC a Najeriya Andrew Yakubu
Talla

Mai shari’a Zainab Abubakar ta amince da bukatar lauyan hukumar EFCC, Salihu Sani, na mallakawa gwamnati makudan kudaden da aka tara ta hanyar da basu kamata ba.

A makon da ya gabata ne aka gano wadanan kudadden da Andrew ya boye a wani gidansa da ke Kaduna.

Sai dai Mista Andrew ya bayyana cewa kudadden kyauta ne da ya samu daga mutane da babu bayanai sunayensu.

EFCC na ci gaba da tsare Andrew Yakubu wanda ya ke ci gaba da yi mata bayanai kan gaskiyar yadda ya tara kudaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.