Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: EFCC ta kwato dala miliyan 151 cikin watanni biyu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, ta sanar da kwato Dala miliyan 151, da kuma naira biliyan 8 daga hannun wadanda suka yi rub da ciki da kudaden gwamnati a cikin watanni biyu kacal.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, Ibrahim Magu
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, Ibrahim Magu
Talla

A wata sanarwa da ya fitar a birnin Legas, ministan yada labaran kasar Alhaji Mohammed ya ce kudaden da aka gano basu hada da akalla dala biliyan 9.2 da aka gano a gidan tsohon shugaban kamfanin man kasar NNPC ba, wato Andrew Yakubu.

Sanarwar gwamnatin tace daga cikin kudaden an samu dala miliyan 136 a wani asusun banki da aka bude da sunan bogi.

Ma’aikatar yada labaran kasar tace, an samu wannan nasarar ce, sakamakon sabbin matakan da aka dauka na baiwa wanda ya tsegunta satar kudaden kashi 5 na kudin da aka kwato.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.