Isa ga babban shafi
Najeriya

EFCC: Buhari ya sake tura sunan Magu a Majalisa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tura sunan Ibrahim Magu zuwa Majalisar dattawan kasar, domin amincewa da shi a matsayin shugaban hukumar EFCC da ke yaki da rashawa a kasar.

Tambarin EFCC hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya
Tambarin EFCC hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya RFI / Pierre Moussart
Talla

A watannin da suka gabata ne Majalisar ta yi watsi da sunan Magu bisa zargin cewa wani rahoton tsaro ya tabbatar da cewa ba zai iya rike wannan matsayi ba saboda wasu dalilai.

Alhaji Sule Ammani Yari, wani magoyi bayan shugaba Buhari, ya ce idan har shugaban ya dage akan Magu to akwai dalili.

Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun ce shugaba Buhari ya dage akan Magu bayan sakamakon binciken da mataimakin shugaban kasa da ministan Shari’a suka gudanar ya tabbbatar da ba ya da laifin rashawa da ake zargin shi.

Shugaba Buhari kuma ya wanke sakataren Gwamnati Babachir David Lawal wanda kwamitin bincikensa da Majalisar Dattijai ta kafa ya bukaci a dakatar da shi tare da hukunta shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.