MTN ya biya Najeriya Naira biliyan 80
Kamfanin sadarwa na MTN ya biya gwamnatin Najeriya Naira biliyan 80 daga cikin tarar Naira biliyan 330 bayan kamfanin ya ki rufe layukan mutane fiye da miliyan biyar da ba su yi rajistar layinkansu ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ministan sadarwa na kasar Adebayo Shittu ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da aka gudanar a birnin Abuja.
An ci tarar MTN Dala biliyan biyar da miliyan biyu kafin daga bisani a rage zuwa Naira biliyan 330 bayan cimma matsaya a tsakanin bangarorin biyu, kuma wannan shi ne karon farko da kamfanin ke fara biyan tarar da aka tsara zai biya a tsawon shekaru uku.
A watan Oktobar 2015 ne hukumar kula da kafofin sadarwa NCC, ta yanke hukunci tare da cin kamfanin tara bisa laifin kin yanke layukan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu