Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Najeriya miliyan 1.7 sun rasa ayyukan yi a watanni 9

Ofishin Hukumar Kididdiga a Najeriya, ya ce matsalar tattalin arziki da kasar ke fama da ita ta sa mutane milyan daya da dubu dari bakwai sun rasa ayyukansu a cikin watanni tara na shekarar 2016.

Birnin Lagos cibiyar kasuwanci a Najeriya
Birnin Lagos cibiyar kasuwanci a Najeriya ©Reuters/Greg Ewing
Talla

Alkalumman Hukumar sun bayyana cewa kafin watan Janairun wannan shekara, yawan wadanda ba su da aikin yi milyan tara ne da dubu hudu da tamanin da takwas, amma kafin karshen watan satumba adadin ya tashi zuwa milyan 11 da kusan dubu 200.

Najeriya dai ta shiga matsalar tattalin arziki ne sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma tsagerun Neja Delta da ke ci gaba da yin ta’adi a yankin mai arzikin fetir da kasar ke dogaro da shi.

Faduwar darajar Naira ma ya taimaka ga matsalolin tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai masana na ganin rungumar kayan da ake samarwa a Najeriya zai taimakawa wajen magance matsalolin ayyukan yi tsakanin ‘Yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.