NCC ta dakatar da karin kudin data a Najeriya
Hukumar da ke sa ido a kan kamfanonin sadarwa ta Najeriya, NCC, ta dakatar da shirinta na kara kudin data ga masu amfani da wayar Salula sakamakon sukar da suke sha daga wurin jama'a.
Wallafawa ranar:
A zantawarsa da RFI Hausa shugaban hukumar ta NCC, Farfesa Umar Garba Dambata, ya ce sun umarci kamfanonin sadarwa kasar su dakatar da karin kudin datar da ya kamata ya soma aiki daga gobe 1 ga watan Disamba, zuwa nan gaba.
Farfesa Umar ya ce daukan matakin zai basu daman tuntubar masu ruwa da tsaki da sauraron ra’ayoyin masu amfanin da layukan salulan.
Kafin wannan mataki Majalisar dattijen Najeriya ta umarci hana Karin, yayin da ‘yan Najeriya ke cewa wani yunkuri ne takaita fadin albarkacin bakinsu a shafukan sadarwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu