Isa ga babban shafi
Najeriya

Manyan kwamandojin sojin Najeriya zasu yi bikin Kirsimeti a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta umurci manyan kwamandojinta, su tafi jihar Barno domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti tare da dakarun su dake bakin daga.

Sojin Najeriya
Sojin Najeriya
Talla

Zalika rundunar, ta bayyana shirin bude wasu manyan hanyoyi da aka rufe a Jihar Barno saboda rikicin kungiyar Boko Haram.

A zantawarsa da sashin Hausa na RFI, daraktan yada labaran rundunar Janar Sani Usman Kukasheka yace, a halin da ake ciki rundunar sojin Najeriya ta kafa sansanoni 14 a cikin dajin Sambisa.

Kukasheka ya ce babban dalilin bawa manyan kwamdojin soji umarnin gudanar da bikin Kirsimeti a Borno, shi ne don karawa sojin da ke bakin daga kwarin gwiwa.

A gefe guda kuma, darakatan yada labaran rundunar sojin ya ce, a wani yanayi da ke nuna ingantar tsaro a yankunan da a baya ke fama da hare haren Boko Haram, za’a bude manyan hanyoyi guda biyu da aka rufe saboda rashin tsaro.

Hanya ta farko it ace wadda ta tashi daga garin Maiduguri zuwa Damasak, sai kuma wadda ta tashi daga Maiduguri zuwa garin Baga.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.