Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan kunar bakin wake sun mutu a Maiduguri

Wasu mata  biyu ‘yan kunar bakin wake sun mutu bayan bama-baman da suka yi damara da su sun tashi a jikinsu gabanin kaddamar da hari a birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya. 

Wata kasuwa da wata mace 'yar kunar bakin wake ta kai wa hari a birnin Maiduguri
Wata kasuwa da wata mace 'yar kunar bakin wake ta kai wa hari a birnin Maiduguri
Talla

Hukumomin jihar sun bayyana cewa, lamarin ya faru da misalin karfe 10:30 na daren jiya agogon kasar a kusa da garejin Muna da ke fama da hare-haren kunar bakin wake a 'yan kwanakin nan.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Victor Isuku ya shaida wa maneman labarai cewa, mutane uku sun samu raunuka bayan tashin bama-baman da ake zargin Boko Haram ce ta shirya.

Tuni dai aka tanadi matakan tsaro a yankin da lamarin ya faru kuma hankulan jama’a sun kwanta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.