Isa ga babban shafi
Najeriya-Maiduguri

Mutane 9 sun rasa rayukansu a Maiduguri

Rahotanni daga Jihar Borno a tarayyar Najeriya sun ce an samu fashewar tagwayen bama-bamai a cikin garin Maiduguri da safiyar yau.

AFP PHOTO
Talla

Bam na farko ya fashe a bakin sansanin ‘yan gudun hijira na Bakkasi da ke kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri, inda kawo yanzu aka tabbatar da mutuwar mutane 6.

Wakilinmu a Jihar Borno Bilyamin Yusuf, ya rawaito mana cewa wani dan kunar bakin wake ne cikin shigar mata ya shiga tsakiyar wasu ‘yan gudun hijira da suka fito bakin sansanin da nufin yin itace, inda ya tada bam din.

Bam na biyu kuma ya tashi ne a gaban ma’ajiyar man fetur na kamfanin NNPC, shima da ke kan hanyar, nesa kadan daga inda na farko ya tashi, inda ya kashe wasu mutane 3 da ke cikin Keke Napep.

Yanzu haka dai mutane 21 da daya ke karbar magani a asibiti.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.