Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

An yi wa sojin Najeriya Kwanton bauna

Rundunar Sojin Najeriya ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun yiwa sojojinsu kwantar bauna akan hanyar Damboa zuwa Maiduguri inda suka kashe fararen hula 6.

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan ayarin sojin Najeriya dake kan hanyar zuwa Maiduguri.
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan ayarin sojin Najeriya dake kan hanyar zuwa Maiduguri. AFP
Talla

Daraktan yada labaran rundunar, Kanar Sani Usman Kukasheka, yace sojojin na rakiyar tawagar motocin sufuri ne lokacin da aka kai musu harin.

Jami’in yace sojojin su 3 sun samu rauni kuma an dauke su zuwa Maiduguri domin kula da lafiyar su.

Daraktan ya bukaci jama’a da su dinga taka tsan tsan, yayin da ya sha alwashin cewar sojojin zasu ci gaba da iya kokarinsu wajen murkushe mayakan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.