Isa ga babban shafi
Najeriya

Babu sojan Najeriya ko daya a hannun 'yan ta'adda-Birgediya Janar Bulama

Wata Kungiyar dake ikirarin 'yantar da Naija Delta da ake kira 'Concerned Militant Leaders' tayi ikirarin kama sojojin Najeriya 24 a Bakassi kuma tace tana rike da su yanzu haka.

Tsagerun yankin Niger Delta a Najeriya
Tsagerun yankin Niger Delta a Najeriya
Talla

Sai dai kuma a zantawarmu da shi Kwamnadan rundunar sojin dake Bakassi, Birgediya Janar Bulama Biu ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewa babu gaskiya cikin ikirarin da suka yi illa shirme da farfaganda.

Ya ce a halin da ake ciki babu wani sojan Najeriya ko daya da yake tsare a hannun wata kungiyar ‘yan ta’adda a yankin.

Birgediya Janar Bulama ya kara dacewa wannan duk bazai sanya su ja da baya ga kokarin kawo karshen matsalar tsaro ba a yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.