Najeriya ta dade da daukan matakan bunkasa arzikinta
Fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buahari ta ce, ko kafin hukumar kididdiga ta tabbatar da koma-bayan tattalin arzikin da kasar ke fuskanta, dama gwamnati ta dauki matakan kawar matsalar.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwar da fadar ta fitar ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan harkar noma da samar da albarkatun karkashin kasa da karban haraji da bunkasa masana’antu da kuma yaki da cin hanci da rashawa har ma da rage yawan kudaden da gwamatin ke kashewa.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da al’ummar Najeriyar ke kukan tsadar rayuwa saboda tabarbarewar tattalin arzikin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu